Duniyar kiɗan Ghana ta shiga jimami bayan rasuwar fitaccen mawaki, ɗan kida kuma jagoran salon highlife, Ebo Taylor, yana da shekaru 90. Iyalan marigayin sun tabbatar da rasuwarsa a ranar Lahadi ta shafin sa na Instagram, ba tare da bayyana musabbabin mutuwar ba, yayin da Kungiyar Mawaka ta Ghana (Musicians Union of Ghana) ta ce ya rasu ne a Asibitin Saltpond.
Mutuwar Taylor ta zo a wani lokaci mai sosa zuciya—kwana guda bayan kaddamar da bikin kiɗa na farko da aka sanya wa suna Ebo Taylor Music Festival, kuma wata guda kacal bayan ya cika shekaru 90. A sanarwar da aka fitar, an bayyana shi a matsayin “gagarumin ginshiki a kiɗan Afirka,” tare da jaddada cewa gadonsa ba zai gushe ba.
A tsawon fiye da shekaru sittin a fagen kiɗa, Taylor ya gina suna ta hanyar haɗa sautin gargajiyar Ghana da jazz, funk, soul da tushen Afrobeat. Ya yi suna tun farko tare da kungiyoyi irin su Stargazers da Broadway Dance Band, sannan a shekarun 1960 ya koma London inda ya yi aiki tare da fitaccen jagoran Afrobeat, Fela Kuti—hadin gwiwar da ta zama tarihi.
Bayan dawowarsa Ghana, Taylor ya jagoranci kungiyoyi da dama kuma ya yi aiki da manyan mawaka. Duk da shahararsa a Yammacin Afirka tun tuni, sunansa ya kara karbuwa a duniya bayan fitar kundin Love and Death a 2010, wanda ya bude kofar manyan ayyuka na gaba. Wakokinsa na tarihi—kamar Heaven, Atwer Abroba da You Need Love—sun ci gaba da rinjayar kiɗan Afirka da na duniya.
Majiyar Labari: TVC NEWS














