Shugaba Trump ya jingina faɗaɗa harin soji kan Iran don ƙarancin makaman tsaron samaniya — rahoto

Rahoton ya ce matakin ya biyo bayan damuwa game da ƙarancin tarin makamai masu linzamin Amurka da taɓarɓarewar lammura a yankin da kuma barazana ga ƙwayenta yankin Gulf.
26 Jul, 2026
An kai wa ma’aikatan jiragen ruwan India hari kusa da mashigar Hormuz

New Delhi ta ba da rahoton cewa wani hari kan wani jirgin dakon kaya na ‘yan kasuwa a Bahar Aswad ya kashe wani ɗan India, yayin da aka kai hari kan wani jirgin ɗauke da iskar gas da ma’aikan jirgin ruwan India 28 a cikin ruwan Iran.
25 Jul, 2026
Iran ta yi watsi da tayin tsagaita wuta da Amurka ta yi mata – rahoto

A cewar rahoton, Tehran ta yi watsi da tayin ne saboda bai warware batun iko da Mashigar Ruwa ta Hormuz ba.
24 Jul, 2026
Ayyukan ‘yan kama-wuri-zauna na Isra’ila na barazana ga ƙoƙarin zaman lafiya a Ƙudus: Turkiyya

“Ankara za ta ci gaba da kare haƙƙin al’ummar Falasɗinu da na birnin Kudus a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa,” in ji Shugaban hukumar Sadarwa na Turkiyya.
24 Jul, 2026

Houthi ta gargaɗi kamfanonin jigilar kaya su guji amfani da tashoshin jiragen ruwa na Saudiyya

Iran ta kashe sojojin Amurka biyu, yayin da Trump ya ba da umarnin kai mata hare-hare

Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin Amurka bayan ta jure dare na bakwai na hare-hare

Amurka ta amince da sayar wa Saudiyya makamai na kusan dala biliyan biyu

Trump ya ce Amurka za ta kai hari kan tashoshin wutar lantarki da gadoji na Iran a makon gobe
14 Jul, 2026
Tsohon Shugaban Iran Ahmadinejad ya musanta rahotannin cewa Isra’ila ta yi ƙoƙarin ɗaukarsa aiki
A cikin wata sanarwa, ofishin Ahmadinejad ya zargi jaridar New York Times da wallafa rahotannin da aka ƙiƙira don yaudarar ra’ayin jama’a da ƙara haddasa rarrabuwar kai a cikin gida a Iran.

14 Jul, 2026
Ministan Tsaron Isra’ila ya ce rusa Gaza yana sa shi ‘nishaɗi’
Ministan tsaron Isra’ila Israel Katz ya ce yana jin daɗin yadda ake lalata yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda ya ba da shawarar kafa matsugunan Yahudawa na dindindin a arewacin Gaza.

13 Jul, 2026
Iran ta kai manyan hare-haren makami mai linzami da jirage marasa matuƙa a Gabas ta Tsakiya
Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran IRGC ta ce ta kai hari kan “sansanonin abokan gaba” a faɗin Bahrain da Kuwait da Jordan a matakin farko na harin ramuwar gayya kan Amurka, inda Iran ɗin ta yi gargaɗin wasu hare-haren na nan tafe.

12 Jul, 2026
Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran ta sanar da rufe Mashigar Ruwan Hormuz ‘sai abin da hali ya yi’
Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran (IRGC) ta ce an dakatar da duk wata jigila a Mashigar Ruwan Hormuz sakamakon wani lamari da ya shafi wani jirgin ruwan kasuwanci.

11 Jul, 2026
Jagoran Addinin Iran ya sha alwashin rama kisan da aka yi wa Ali Khamenei
Khamenei ya ce ramuwar gayyar ba ta dogara kan niyyarsa ko ta ko wane jami’in Iran ba.

11 Jul, 2026
Trump ya yi gargaɗin cewa Amurka za ‘hallaka da lalata’ Iran idan Tehran ta kai masa hari
“An riga an ba da umarni, kuma rundunar sojin Amurka tana a shirye, kuma tana da niyya da iko, na tsawon shekara ɗaya, wanda za a iya tsawaitawa, ta hallaka da kuma lalata gaba ɗaya dukkan ƙasar Iran,” a cewar Trump .

10 Jul, 2026
Masu shiga tsakani suna fafutukar kwantar da tankiya tsakanin Amurka da Iran
Kasar Qatar, Saudiyya, Pakistan da Masar suna gudanar da tattaunawa ta wayar tarho mai zurfi da kasashen Amurka da Iran domin kwantar da sabuwar takaddamar da ta barke, da samar da hanya ga sabuwar tattaunawa ta kwararru kan yarjejeniyar nukiliya

9 Jul, 2026
Turkiyya da Iran sun tattauna kan halin da yankin ke ciki, da tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran
Hakan Fidan da Abbas Araghchi sun tattauna kan abubuwan da suke faruwa, da matsayin tsagaita wuta, a cewar majiyoyin harkokin wajen Turkiyya.

9 Jul, 2026
Akwatin gawar Khamenei ya isa Mashhad a yayin da Iran ke shirin taron jana’iza na ƙarshe
Iran ta shirya gudanar da taron jana’izar Jagoran Addini na ƙasar da aka kashe, Khamenei, bayan tarukan da aka yi da masu makoki suka halarta.

7 Jul, 2026
Iran ta harba makamai masu linzami kan jiragen ruwan kasuwanci a Mashigar Hormuz: Rahoto
Jami’an tsaron Rundunar juyin-juya-hali na Iran sun harba akalla makamai masu linzami biyu kan jiragen ruwan kasuwanci da ke ratsawa ta Mashigar Hormuz.



