Galatasaray ta samu gagarumar nasara da ci 5-2 a kan Juventus a wasan zagaye na farko, inda Noa Lang da Gabriel Sara suka taka muhimmiyar rawa. Sara ne ya fara jefa ƙwallo minti 15 da fara wasa, amma Juventus ta rama nan da nan ta hannun Teun Koopmeiners.
Juventus ta ƙara ƙwallo ta biyu kafin hutun rabin lokaci, lamarin da ya sa ta shige gaba. Sai dai bayan dawowa daga hutun, Galatasaray ta sauya fasalin wasa, inda Lang ya rama ƙwallo, sannan Davinson Sanchez ya ƙara ta uku daga ƙwallon da Sara ya shirya.
Al’amura sun kara dagulewa ga Juventus bayan an bai wa Juan Cabal jan kati minti 67, abin da ya rage musu ‘yan wasa zuwa 10. Galatasaray ta yi amfani da damar, inda Lang ya ƙara wata ƙwallo, kafin Sacha Boey ya kammala jerin ƙwallaye da ta biyar.
Za a buga zagaye na biyu a Turin ranar 25 ga Fabrairu.
Majiyar Labari: TRT WORLD














