Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da komawarsa Jam’iyyar APC a hukumance. An sanar da sauya shekar ne a wani taro da aka gudanar ranar Litinin a gidan gwamnati, inda fitattun ‘yan jam’iyyar suka halarta don nuna goyon baya da maraba da sabon ɗan jam’iyya.
Taron ya samu halartar mataimakin shugaban majalisar dattijai Sanata Barau Jibrin, tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, Sanata Kawu Sumaila, A.A. Zaura da shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas, kamar yadda bidiyoyi suka nuna a kafafen sada zumunta.
Sauya shekar ta Abba Kabir ta zo ne bayan makonni ana hasashen hakan, musamman bayan bayyana ɓaraka tsakaninsa da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. A jawabinsa, gwamnan ya jaddada kudirinsa na ci gaba da tafiya da matasa a cikin gwamnatinsa tare da alkawarin ganin an samu canji da haɗin kai a Kano.
Tsohon gwamna Ganduje ya ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin sabon jagoran APC a jihar, yayin da Sanata Barau ya bukaci duk magoya bayan jam’iyyar da su mara masa baya.














