Afirka

Gwamnatin Ghana ta ba da umarnin sarrafa kashi 50 cikin 100 na koko a cikin gida

Rahotani daga ƙasar sun ce ministan kuɗin Ghana Dakta Cassiel Ato Forson ne ya bayyana hakan ranar Alhamis bayan wani zaman gaggawa da majalisar zartarwar ƙasar ta yi domin magance matsalolin da fannin noman koko ke fuskanta a ƙasar.

Newstimehub

Newstimehub

13 Feb, 2026

2026 02 12t173241z 2108413956 rc23jja8wsot rtrmadp 3 cocoa ghana farmers

Gwamnatin Ghana ta ba da umarnin a riƙa sarrafa aƙalla kashi 50 cikin 100 na kokon da ake nomawa a cikin ƙasar daga kakar shekarar 2026 da 2027.

Ministan kuɗin Ghana Dakta Cassiel Ato Forson ne ya bayyana hakan ranar Alhamis bayan wani taron gaggawa da majalisar zartarwar ƙasar ta yi domin magance matsalolin da fannin noman koko ke fuskanta a ƙasar.

Ministan kuɗin ƙasar ya bayyana cewa majalisar zartarwar ƙasar ta kuma ba da umarnin farfaɗo da muhimman kamanonin gwamnati biyu —kamfanin siyan kayayyaki (PBC) da kamfanin sarrafa koko (CPC) — nan-take.

“Za a farfaɗo da kamfanin ƙasa na saiyan kayayyaki PBC domin ya fara aiki gadan-gadan ya kuma zama kamfanin da ke kan gaba wajen siyan lasisi a fannin koko nan take ,” kamar yadda Dakta Ato Forson ya bayyana.

Farfaɗo da kamfanin PBC na zuwa ne a wani muhimmin lokaci inda kamfanonin masu sayen lasisi suke bin kamfanin COCOBOD na gwamnati kimanin sedi biliyan GH¢2.04 , inda wasu manoma ba su samu an biya su ba tun watan Nuwamban shekarar 2025.

Majalisar zartarwar ta kuma ba da umarnin cewa a ware sauran koko na kakar shekarar 2025-2026 ta yanzu domin sarrafawa a cikin gida.

Umarnin zai fara aiki ne nan take kuma wata alama ce ta jajircewar gwamnatin ƙasar kanm sarrafa ababen da ake samarwa a cikin gida da kuma samar da ayyukanyi a fannin koko.