Gwamnatin Nijeriya ta fara wani shirin bayar da tallafin kuɗi na Naira 50,000 duk wata ga gidaje masu ƙaramin ƙarfi, domin rage musu raɗaɗin hauhawar tsadar rayuwa.
Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Bernard Doro, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Abuja.
Doro ya ce shirin bayar da tallafin gaggawa da daidaita tattalin arziki na ƙasa (NERSI) wani shiri ne da shugaban ƙasa ya ƙaddamar, da nufin tallafa wa miliyoyin ’yan Nijeriya masu rauni ta fuskar tattalin arziki.
Ya bayyana cewa an ƙirƙiro shirin ne domin daƙile matsalar hauhawar farashin abinci da ake fuskanta a duniya da kuma ƙarin kuɗin kayan masarufi, waɗanda ke ci gaba da jefa matsin lamba kan kuɗaɗen shigar iyalai.
“Ƙarƙashin wannan shiri, waɗanda suka cancanci cin gajiyarsa za su riƙa samun Naira 50,000 duk wata, domin taimaka musu wajen biyan buƙatun yau da kullum da kuma rage musu tsadar rayuwa,” in ji shi.
Ministan ya ce za a riƙa nazarin shirin lokaci zuwa lokaci domin dacewa da sauye-sauyen farashin rayuwa, inda ya ƙara da cewa za a sanar da waɗanda ke cin gajiyarsa kai tsaye kafin yin duk wani sauyi.
A cewarsa, ma’aikatar tana haɗin gwiwa da kamfanonin samar da kuɗi ta intanet da ke da lasisi, domin tabbatar da cewa ana biyan kuɗaɗen cikin tsaro, a kan lokaci kuma cikin gaskiya da riƙon amana.
Ya bayyana cewa waɗanda suka cancanci tallafin za su riƙa samun saƙonnin kar-ta-kwana daga kamfanonin da ke gudanar da biyan kuɗin, domin neman izininsu kafin a tura kuɗaɗen kai tsaye zuwa asusun bankunansu ko walat ɗin kuɗi na wayoyinsu.
Doro ya jaddada cewa ba a buƙatar waɗanda suka cancanci tallafin su cike takardar neman shiga shirin, su biya kuɗi ko su yi rajista ta hannun wani wakili domin samun tallafin.
Ya kuma gargaɗi ’yan Nijeriya da su yi hattara da ’yan damfara, inda ya buƙace su da kada su bayyana lambobin sirrinsu na katin banki (PIN) ko lambobin tantance asusun banki (BVN) ga kowa.

















