Zanga-zanga ta ɓarke ranar Lahadi a faɗin ƙasar Iran bayan sanarwar da aka fitar cewa Amurka da Isra’ila sun kashe Jagoran Addini Ali Khamenei a hare-haren soji da suka kai ƙasar.
Lamarin ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin zaman zulumi kuma ya jawo kakausan martani daga cikin ƙasar Iran.
Tun da farko gidan talbijin na Iran ya tabbatar da mutuwar Khamenei a hare-haren Amurka da Isra’ila, inda ya bayyana cewa Jagoran Addini na “Juyin-juya-halin Musulunci ya yi shahada.”
Kazalika gwamnatin ƙasar ta sanar da makokin kwana 40 tare da bayar da hutun kwana bakwai.

Kafofin watsa labaran Iran sun ce masu zanga-zangar da ke riƙe da tutocin ƙasar Iran sun taru a cibiyoyin zanga-zanga a biranen ƙasar inda suke bayyana alhininsu.
A Tehran, ɗaruruwan mutane sun taru a Dandalin Inkilap, inda suke riƙe da tutocin ƙasar da fastocin Khamenei, inda suka riƙa Allah wadai da Amurka da Isra’ila.
A birnin Qom, ɗaruruwan mutane sun taru a Hubbaren Hazrat Masume domin yin tur da hare-haren.














