Afirka

Issa Tchiroma Bakary ya yi iƙirarin lashe zaɓen shugaban ƙasar Kamaru

Ɗan takarar jam’iyyar hamayya Issa Tchiroma Bakary ya yi kira ga Paul Biya ya amsa shan kaye ko da yake gwamnati ba ta ce uffan ba game da iƙirarin da ya yi na lashe zaɓen shugaban ƙasar Kamaru.

Newstimehub

Newstimehub

14 Oct, 2025

2025 10 14t051109z 1 lynxnpel9d05c rtroptp 3 cameroon election

Ɗan takarar jam’iyyar hamayya a Kamaru Issa Tchiroma Bakary ranar Litinin da tsakar dare ya yi iƙirarin lashe zaɓen shugaban ƙasar wanda aka gudanar ranar Lahadin da ta gabata, sannan ya yi kira ga Paul Biya ya amsa shan kaye tare da “martaba gaskiyar da ta bayyana ta hanyar masu zaɓe”.

“Nasarar da muka samu a bayyane take. Dole a amshe ta,” a cewar Tchiroma a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook daga garinsu na Garoua.

“Mutane sun zaɓi wanda suke so. Kuma dole a mutunta hakan.”

Tchiroma Bakaray, mai shekara 76, shi ne tsohon mai magana da yawun gwamnati kuma tsohon minita, wanda ya raba gari da Paul Biya a farkon shekarar nan inda ya ƙaddamar da gagarumin yaƙin neman zaɓe da ya samu karɓuwa daga ɗimbin jama’a da kuma wani ɓangare na ‘yan adawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Ko da yake an amince a riƙa bayyana sakamakon zaɓe, sai dai kotun tsarin mulkin Kamaru ce kaɗai take da alhakin sanar da sakamakon ƙarshe, kuma ba a yarda “kowa ya yi gaban kansa ba”.