Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun dakatar da bayar da biza ga duk wani Ba’amurke da ke son shiga ƙasar, a cewar majiyoyin diflomasiyya da kamfanin dillancin labarai na ƙasar, ANP.
Majiyoyin sun bayyana cewa matakin ya nuna ikon kai da ’yancin diflomasiyyar Nijar, tare da jaddada cewa ƙasar ba za ta lamunci raini ko matsin lamba daga kowace ƙasa ba.
Wannan mataki na zuwa ne bayan Amurka ta sanar, a ranar Talata 16 ga Disamba, faɗaɗa jerin ƙasashen da ta dakatar wa bayar da bizar shiga ƙasarta, ciki har da Nijar, Mali da Burkina Faso — ƙasashen ƙawancen Sahel (AES).
A cewar gwamnatin Trump, an ɗauki matakin ne bisa zargin rashin isassun bayanan tantance matafiya, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a Afirka.
Tun a watan Oktoba, Amurka ta ƙara kuɗin bizar shiga ƙasar daga dala $5,000 zuwa $15,000 ga ’yan wasu ƙasashen Afirka, saboda zargin karya sharuddan zaman biza.
Masana na ganin matakin ramuwa da Nijar ta ɗauka na iya shafar haɗin gwiwar diflomasiyya, tattalin arziki da musayar ilimi tsakanin ƙasashen biyu, yayin da ake ci gaba da sanya ido kan yadda rikicin zai kaya.














