Sabbin bayanai daga Abuja sun nuna cewa wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin a tura tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), zuwa gidan yarin Kuje tare da ɗansa da Hajiya Asabe Bashir na Kamfanin Rahamaniyya Properties, har sai an kammala sauraren bukatar belin da suka nema.
Alkali Emeka Nwite ne ya bayar da wannan umarni yayin sauraron ƙarar, bayan lauyan EFCC, Kelechi Ekele (SAN), ya nuna adawa da bukatar belin da lauyan Malami ya gabatar. EFCC na tuhumar Malami da wasu kan tuhume-tuhume 16 da suka shafi haɗin baki wajen ɓoye kuɗaɗen haram, hakanan amfani da kamfanoni da asusun banki don wawure biliyoyin naira, sayen kadarori da ajiye kuɗi a matsayin jingina.
An ce wasu daga cikin zargin sun faru ne a lokacin da Malami ke rike da mukamin Babban Lauyan Tarayya. Duk da haka, su duka sun musanta zarge-zargen. Ana sa ran ci gaba da sauraron ƙarar a zaman kotu na gaba.














