Duniya

Kotu Ta Samu Mutane 10 Da Laifi Kan Bata Sunan Brigitte Macron Ta Hanyar Dabarun Intanet

Wata kotu a birnin Paris ta samu mutane 10 da laifi saboda yada karya da cin zarafi kan Brigitte Macron, matar shugaban Faransa, inda aka yanke musu hukunci daban-daban kan laifin cin zarafi ta yanar gizo.

Newstimehub

Newstimehub

6 Jan, 2026

RTT4DA3I2VKUHLAK6UHJDQVHJQ e1767683858840

Wata kotu a Paris ta tabbatar da cewa mutane 10 sun yi amfani da kafafen sada zumunta wajen yada ƙarya cewa Brigitte Macron “namiji ce aka haifa” tare da yin maganganun batanci game da ita da mijinta, Shugaba Emmanuel Macron.

Daga cikin waɗanda aka samu da laifi, akwai maza takwas da mata biyu, kuma kotu ta ce kalaman da suka yi ya kai matakin cin mutunci, ƙarya da kuma tayar da ƙiyayya. Daya daga cikinsu ya samu hukuncin zaman gidan yari na watanni shida ba tare da sassauci ba, yayin da wasu suka samu hukuncin da aka dakatar, tarar kuɗi da kuma tilasta shiga horo kan batun cyber-harassment. Wasu kuma an hana su amfani da kafafen sada zumuntar da suka aikata laifin a kai.

Macron da matarsa sun dade suna fuskantar irin waɗannan rohotanni marasa tushe, ciki har da batun cewa an haife ta da suna daban. Duk da sun daɗe suna yin shiru, yanzu sun fara ɗaukar mataki ta fuskar shari’a, ciki har da shari’ar da suke yi a Amurka kan bata suna.

Brigitte Macron ta bayyana a tattaunawa da TF1 cewa tana fafutuka ne domin zama misali ga sauran wadanda ke fuskantar cin zarafi ta yanar gizo, musamman matasa. Ta ce lamarin ya kai ga har wasu sun yi ƙoƙarin canza bayanan harajinta a intanet.

Wannan hukunci ya zo ne a lokacin da ake ta takaddama a Turai da Amurka kan iyakar ‘yancin magana da yaƙi da labaran ƙarya da cin zarafi a intanet.

Majiyar Labari: REUTERS