Emine Erdogan ta gana da Kwamishinan Janar na UNRWA, Philippe Lazzarini, a Ankara ranar Alhamis, inda aka tattauna batun tallafa wa ’yan gudun hijirar Falasɗinawa. Bayan taron, Lazzarini ya sanar da cewa UNRWA za ta buɗe ofishi a Ankara cikin ’yan makonni bayan kammala yarjejeniya da gwamnatin Turkiyya.
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da UNRWA ke fuskantar matsanancin ƙarancin kuɗi, lamarin da ya tilasta ta korar ma’aikata 571 a Gaza. Lazzarini ya ce duk da ƙalubale da matakan da Isra’ila ke ɗauka domin rage ayyukanta, UNRWA na ci gaba da tallafa wa ’yan gudun hijirar Falasɗinawa a yankuna daban-daban.













