Nijeriya

Kotu ta umurci Birtaniya ta biya fam miliyan 420 diyyar kisan masu haƙar kwal 21 a Enugu

Babbar Kotun Tarayya da ke Enugu ta umurci Gwamnatin Birtaniya ta biya fam miliyan 420 ga iyalan masu haƙar kwal 21 da aka kashe a Iva Valley Coal Mine a shekarar 1949, tare da neman gafara a hukumance.

Newstimehub

Newstimehub

6 Feb, 2026

2026 02 04t114150z 1277181660 rc2zeja73t8o rtrmadp 3 usa trump epstein mandelson

Shekaru kusan 76 bayan faruwar wani mummunan lamari a tarihin mulkin mallaka a Nijeriya, iyalan wasu masu haƙar kwal da aka kashe a Enugu sun samu abin da suke jira tun tuni. A ranar Alhamis, Babbar Kotun Tarayya da ke Enugu ta yanke hukunci kan kisan gillar da sojojin Birtaniya suka aikata a shekarar 1949, inda ta umurci Gwamnatin Birtaniya da ta biya diyya mai tsoka ga iyalan waɗanda abin ya shafa.

Mai shari’a Anthony Onovo ya bayar da umarnin cewa Gwamnatin Birtaniya ta biya fam miliyan 20 ga iyalan kowane ɗaya daga cikin masu haƙar kwal 21 da aka kashe a Iva Valley Coal Mine, Enugu, ranar 18 ga Nuwamba 1949. Hakan ya kai jimillar diyya zuwa fam miliyan 420.

Kotun ta bayyana cewa masu haƙar kwal ɗin sun shiga zanga-zanga ne bisa mawuyacin yanayin aiki, nuna wariyar launin fata wajen albashi da kuma kuɗin da ba a biya su ba, ba tare da amfani da tashin hankali ba. Sai dai jami’an mulkin mallaka sun mayar da martani da harbin bindiga, lamarin da ya yi sanadin mutuwar 21 tare da jikkata wasu 51.

Alƙalin ya bayyana kisan a matsayin wanda ya saɓa wa doka da kisan gilla, tare da tauye haƙƙin rayuwa, inda ya ɗora cikakken alhaki a kan gwamnatin mulkin mallaka ta Birtaniya. Kotun ta kuma umurci Birtaniya da ta nemi gafara a hukumance ta hanyar diflomasiyya.

Ƙarar ta samu ne ta hannun mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Greg Onoh, wanda ya nemi a tabbatar da laifin, a nemi gafara da kuma biyan cikakkiyar diyya ga iyalan mamatan. Rahotanni sun nuna cewa babu lauyan da ya wakilci wasu daga cikin waɗanda aka kai ƙarar a lokacin shari’ar.

Majiyar Labari: TRT Hausa