Matashin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal ya mayar da martani kan sukar da kocinsa Hansi Flick ya yi kan halayyar ‘yan wasan ƙungiyar da ke kawo musu matsala.
Flick ya faɗa a wata tattaunawa cewa, rashin nasarar da suka yi a wasansu da Rayo Vallecano ranar Lahadi yana “ganin ba matsalar rashin fara kakar bana da karsashi kamar bara ba ce”.
Ya ce, “Maganar ita ce ta ji-ji-da-kai tsakanin ‘yan wasanmu a wajen fili. Bayan yin canjaras, za ka yi takaici; amma a ƙarshe dole ka nemi yin nasara [a gaba].”
Bayan wannan kalaman ne, idanu suka koma kan Lamine Yamal saboda yadda tauraruwarsa ke ƙara haskakawa a tawagar Barcelona da ma ta Sifaniya.
Martanin Yamal














