Masu bincike sun gano wani muhimmin abin tarihi a Tsibirin Muna da ke Kudancin Sulawesi a ƙasar Indonesia, inda aka gano wani zanen hannu a cikin kogo da ake kyautata zaton shi ne mafi tsohon zanen kogo a duniya. 
Binciken, wanda aka wallafa a mujallar Nature, ya nuna cewa wannan zane yana da akalla shekaru 67,800, lamarin da ke ƙara nuna cewa mutane sun riga sun fara yin fasaha tun ƙarni-ƙarni masu nisa da suka wuce. Wannan ganowa ta ƙara haske kan tarihin ɗan’adam da yadda suka fara bayyana tunaninsu ta hanyar zane.















