Shafukan sada zumunta sun kaure da muhawara bayan wasu ‘yan Zambiya sun nuna sha’awa game da wani shahararren tufafin Ghana—fugu—bayan Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya kai ziyara Lusaka yana sanye da shi. Wannan ya sa ‘yan Ghana da dama suka rika wallafa hotunansu suna sanye da fugu domin nuna muhimmancinsa a al’adarsu.
Fugu, wanda aka fi sani da Batakari, tufafi ne na gargajiya daga arewacin Ghana, musamman a tsakanin Dagomba, Konkomba, Mamprusi, Gonja da sauran kabilu. Ana yin sa ne da auduga mai kauri, ana sakawa a tsiri-tsiri da aka saƙa da hannu, a dinke su su zama tufafi masu sako-sako irin na tunic.
Peter Adagwine, dan shekara 44 daga Tamale, ya ce ya taso yana sanye da fugu tun yana yaro. “A makarantar sakandare da ke Tamale, wajibi ne kowa ya mallaki fugu domin haɗa kai da al’adu,” in ji shi. Yanzu yana aiki a Accra a matsayin ma’aikacin gwamnati.
Duk da cewa kente shi ne tufafin Ghana da ya fi shahara a duniya—har ma UNESCO ta saka shi cikin jerin gado na al’adu—fugu ma na da zurfin ma’ana. Yana wakiltar asali, haɗin kai da gadon al’adu, kuma ana sanya shi a lokutan bukukuwa, aure, da suna. Sarakuna da dattawa na sanya fugu mai kwalliya don nuna ikon mulki da sarauta.

A tarihi, mafarauta da jarumai ne ke sanya fugu saboda ƙarfinsa da ma’anarsa ta ruhaniya. A yau kuma, shugabannin siyasa a Ghana—ciki har da shugabannin ƙasa—sun dade suna sanya fugu a manyan taruka.
“Yanzu fugu ya zama na zamani kuma kowa yana amincewa da shi. Mata ma suna dinka tufafi daga audugar. Marigayi Jerry John Rawlings da Shugaba John Mahama sun taka rawa wajen yaɗa sa,” in ji Adagwine.
Launuka da zane-zanen fugu na da ma’ana: shuɗi (indigo) na nuni da juriya da hikima, baƙi kuma kariya da ikon kakanni. Tsarinsa mai faɗin kafadu da gefuna yana ba da ‘yancin motsi.
A bangaren tattalin arziki, yin fugu sana’a ce: maza na sarrafa injinan saƙa, mata kuma na rini da kammala audugar da launukan tsire-tsire. Wannan na taimakawa dorewa, sahihanci da samar da ayyukan yi.
A yau, fugu ya wuce iyakokin yanki, ya zama alamar alfaharin Ghana, yana haɗa gargajiya da zamani—shaida ce ta fasahar Ghana, asalin ƙasa, da dogaro da kai.
Majiyar Labari: TRT AFRIKA














