Hukumar Kula da Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta bayyana cewa aƙalla mutane 33 sun mutu, yayin da wasu 33 suka jikkata sakamakon hatsarin da ke da alaƙa da wutar lantarki a fadin ƙasar cikin watanni uku na uku na shekarar 2025. Rahoton ya nuna cewa an samu jimillar hatsari 57 a wannan lokaci.
Cibiyoyin lantarki na Ikeja da Kano ne suka fi fuskantar hadurra, inda kowannensu ya samu hatsari 10. Ikeja ta yi asarar rayuka huɗu tare da jikkatar mutane shida, yayin da Kano ta rasa mutane shida tare da jikkatar huɗu. Sauran wuraren da aka samu hadurra sun haɗa da Abuja, Jos, Aba, Port Harcourt, Enugu, Yola, Eko, Kaduna da TCN.
NERC ta danganta mafi yawan mutuwar da raunuka ga sakacin aiki, rashin bin ƙa’idojin tsaro, da kuma aikin da ba masu lasisi suka yi. Tsinkewar waya, kuskuren ma’aikata, da shiga wuraren lantarki ba tare da izini ba na daga cikin manyan dalilan afkuwar hadurran.
Hukumar ta ce ta fara bincike kan dukkan lamarin, tare da shirya taron masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa matakan kariya da hana sake faruwar irin waɗannan hadurra a nan gaba.














