Abba Atiku Abubakar, ɗa ga tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar, ya shiga jam’iyyar APC bayan ya fice daga PDP.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ne ya bayyana hakan ta shafinsa na Facebook, inda ya wallafa hotunan karɓar Abba Atiku da tawagarsa a hukumance.
Sanata Barau ya ce an karɓi Abba Atiku zuwa APC ne a zauren Majalisar Dattawa ta ƙasa, a gaban manyan jiga-jigan jam’iyyar, ciki har da Mataimakin Shugaban APC na shiyyar Arewa Maso-Gabas, Kwamared Mustapha Salihu, da wasu manyan masu ruwa da tsaki.
Ya ƙara da cewa Abba Atiku ya sanar da murabus dinsa daga jam’iyyar PDP tare da bayyana aniyarsa ta mara wa APC baya da kuma goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
A nasa jawabin, Abba Atiku ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne sakamakon kyakkyawan jagoranci da irin rawar da Sanata Barau Jibrin ke takawa a siyasar ƙasa. Ya kuma bayyana shirinsa na yin aiki tare da jam’iyyar domin tabbatar da nasarar wa’adi na biyu ga Shugaba Tinubu.
Abba Atiku ya bukaci dukkan mambobin ƙungiyarsa ta Haske Atiku, wadda yanzu ya ce ta koma Haske Tinubu, da su shiga APC tare da haɗa ƙarfi wajen samun nasara a 2027.
A ƙarshe, Sanata Barau Jibrin ya tabbatar wa Abba Atiku da magoya bayansa cewa APC za ta ba su cikakken goyon baya da damar da ya dace a cikin jam’iyyar.














