Sojojin Nijeriya sun samu nasarar ceto mutum 18, ciki har da ƙananan yara biyu, daga hannun ‘yanfashin teku da suka yi garkuwa da su a yayin da suke tafiya a kwalekwale daga Nijeriya zuwa Kamaru. Rundunar ta ce lamarin ya faru ne a gaɓar tekun Kombo Fishing Port da ke yankin Kamaru.
A cewar mataimakin mai magana da yawun Birged ta 13, Manjo Yemi Sokoya, dakarun da ke Ikang sun bi sawun ‘yanfashin tekun bayan sace fasinjojin, inda aka yi musayar wuta har sai da ɗaya daga cikin kwalekwalensu ya kife. Daga bisani ‘yanfashin suka tsere zuwa daji, suka bar dukkan mutanen da suka yi garkuwa da su, waɗanda aka ceto su lafiya ba tare da wani rauni ba.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














