Ajanda Najeriya

NCC da CBN Sun Kafa Dokar Maidowa Kuɗin Airtime da Data da Suka Gaza

NCC da CBN sun cimma matsaya kan sabon tsari da zai tilasta maidowa kwastomomi kuɗin airtime ko data da suka gaza cikin daƙiƙa 30.

Newstimehub

Newstimehub

10 Jan, 2026

NCC and CBN 1 1 780x470 1 664x400 1

Mutane da dama a Nijeriya sun dade suna korafi kan cire kuɗin airtime ko data ba tare da samun abin da suka saya ba, lamarin da ke janyo fushi da rashin amincewa da kamfanonin sadarwa da bankuna. Don kawo ƙarshen wannan matsala, Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) tare da Babban Bankin Nijeriya (CBN) sun ƙaddamar da sabon tsarin haɗin gwiwa da zai kare haƙƙin masu amfani da sadarwa.

A cewar NCC, sabon tsarin ya tanadi cewa duk wanda aka cire masa kuɗi amma bai samu airtime ko data ba, za a mayar masa da kuɗinsa cikin daƙiƙa 30, sai dai idan cinikin yana matsayin pending, wanda a irin wannan yanayin maidowa kuɗin zai iya ɗaukar awa 24. Tsarin ya kuma wajabta wa kamfanonin sadarwa da bankuna bayyana wa kwastomomi ta SMS ko ciniki ya yi nasara ko ya gaza.

Hukumar ta ce an cimma wannan matsaya ne bayan shawarwari da suka haɗa NCC, CBN, kamfanonin sadarwa, bankuna da sauran masu ruwa da tsaki. Rahotanni sun nuna cewa sama da Naira biliyan 10 an riga an mayar wa kwastomomi sakamakon irin waɗannan matsaloli. Ana sa ran sabon tsari zai fara aiki daga 1 ga Maris, bayan kammala amincewa da shirye-shiryen fasaha.

Majiyar Labari: TVC NEWS