Gwamnatin Nijeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun cim ma wata babbar yarjejeniya ta kasuwanci da ta kai ga soke haraji kan kayayyaki fiye da 13,000 da ake cinikayya da su tsakanin ƙasashen biyu. Nijeriya ta cire haraji kan kayayyaki 6,243 da ake shigowa da su daga UAE, yayin da ita ma UAE ta soke haraji kan kayayyaki 7,315 da ake kai mata daga Nijeriya.
Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta ce wannan mataki ya biyo bayan rattaba hannu kan Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki (Nigeria–UAE Comprehensive Economic Partnership Agreement) a Janairu 2026, wacce ke da nufin bunƙasa kasuwanci, jawo sabbin jarin waje da kuma rage dogaro da man fetur a tattalin arzikin Nijeriya.
A karkashin yarjejeniyar, Nijeriya ta cire haraji kan kaso 63 cikin 100 na kayayyaki, inda kaɗan ne kawai suka rage ba tare da rangwame ba. A bangaren UAE kuwa, an soke haraji kan dubban kayayyaki nan take, yayin da za a ci gaba da cire sauran a cikin shekaru uku zuwa biyar masu zuwa.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a gaban Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da Shugaban UAE Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan, inda Ministoci daga ɓangarorin biyu suka tabbatar da cewa wannan sabon mataki zai buɗe ƙofofi ga ƙarin zuba jari, ƙarfafa fitar da kaya da samar da ayyukan yi.













