A wasan da ya cika da tashin hankali da armashi a birnin Casablanca, tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta nuna jajircewa da jarumta bayan ta doke Masar a bugun fenareti, ta haka ta kwashe lambar yabo ta tagulla a gasar AFCON, abin da ya sanya magoya baya yin alfahari da ƙungiyar duk da ba su kai wasan ƙarshe ba.
Bayan wasan minti 90 ya kare babu ci a filin Mohammed V, an tafi bugun fenareti inda Nijeriya ta yi nasara da ci 4-2. Golan Stanley Nwabali ya zama gwarzo bayan ya kaɗe fenareti biyu ciki har da na Mohamed Salah. Duk da ƙwallayen da Paul Onuachu da Ademola Lookman suka zura amma aka soke su ta VAR, Super Eagles ta nuna ƙarfi, inda Shugaba Bola Tinubu ya yabawa tawagar, yana cewa lambar tagullar ta yi kama da zinare.














