Atiku ya sha alwashin mayar da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban Nijeriya a 2027

Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da ‘yan jarida a ranar Laraba, inda ya ce duk wanda ya sace kuɗaɗen da aka ware domin tallafin man fetur za a tilasta masa mayar da su idan ya hau mulki.
20 Aug, 2026
Sufeto Janar na ‘Yansandan Nijeriya ya yi gargaɗi kan ɗora wa mutane laifuka bisa ƙabila ko addini

Disu ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabin buɗe taron Tsaro na Shiyyar Arewa Maso Yamma a Gusau inda ya yi kira da a ɗauki matakan yaƙi da rashin tsaro na yankin bisa amfani da bayanan sirri, goyon bayan al’umma.
20 Aug, 2026
An buɗe yaƙin neman zaɓen shugaban Nijeriya na 2027 a hukumance

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar 16 ga Janairu, 2027 a matsayin ranar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Ƙasa, abin da ya sa yau ta zama ranar fara kamfen a hukumance, kamar yadda jadawalin zaɓen ya tanada.
19 Aug, 2026
Tsohon Shugaban Nijeriya Jonathan ya yi gargaɗi kan yadda gwamnoni ke tarewa a jihohin da ake zaɓe

Jonathan ya bayyana wannan al’amari a matsayin mara kyau, inda ya ce idan ba a shawo kansa ba, yana iya zama barazana ga tsarin dimokuradiyyar Najeriya tare da haifar da mummunan tasiri na dogon lokaci ga dorewar dimokuradiyya.
18 Aug, 2026

Ana zargin Lakurawa da kashe aƙalla mutum 28 a masallaci a Sokoto

Akwai ramukan haƙar ma’adanai fiye da 4,000 da aka yi watsi da su a Filato — Alake

Manoma biyar sun rasu bayan kwale-kwale ya kife a Jihar Neja ta Nijeriya

‘Yansandan Nijeriya sun kama wani mutum kan zargin watsa wa matarsa fetur da cinna mata wuta

Sake cin zaɓen gwamnan Osun tabbaci ne cewa dimokuraɗiyya za ta ci gaba da bunƙasa a Nijeriya—Tinubu
15 Aug, 2026
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke ketare su zuba jari a Nijeriya
Shugaban Tinubu ya yi kira ga ‘yan ƙasar da ke ƙetare su haɗa kai wajen zuba jari maimakon rarraba jarinsu kuma su tabbatar da cewa na an bi da jarinsu yadda ya dace bisa jagorancin ƙwararru.

14 Aug, 2026
Tinubu ya yi alƙawarin farfaɗo da matatun man Nijeriya da suka jima ba sa aiki yadda ya kamata
Shugaban ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Alhamis lokacin da ya karɓi shugabannin Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (NUPENG) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

13 Aug, 2026
Shugabannin addinai a Nijeriya sun sa hannu kan yarjejeniyar inganta zaman lafiya da fahimtar juna
Fiye da shugabannin addinin Musulunci da Kiristanci 50 sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin addinai a Abuja, inda suka ƙaddamar da wata sabuwar ƙungiya da za ta yi aiki wajen inganta zaman lafiya da fahimtar juna.

13 Aug, 2026
An gano gawawwaki 9 a Jihar Neja ta Nijeriya, kwanaki bayan ceto mutane 308 da aka yi garkuwa da su
Ana zargin ’yanbindiga ne suka kashe mutanen yayin da suke tafiya a kan hanyar Wawa-Lumma da ke Ƙaramar Hukumar Borgu ta jihar.

12 Aug, 2026
Kaduna, Sokoto, Zamfara da wasu jihohin Nijeriya 10 na fuskantar barazanar ambaliya – NiMet
Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata ta lissafo jihohin Nijeriya 13 a matsayin jihohin da ke cikin babban haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa.

11 Aug, 2026
‘Yansandan Nijeriya 10 sun rasa rayukansu a musayar wuta da mahara a arewacin ƙasar, in ji hukumomi
Wata mummunar musayar wuta tsakanin wasu mahara da ke ɗauke da makamai da jami’an tsaron Nijeriya ta yi sanadiyyar mutuwar jami’ai 10 da mahara 17 a wani ƙauye a Masarautar Zuru a kan iyakar jihohin Kebbi da Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.

11 Aug, 2026
‘Yan Nijeriya sun kashe Naira tiriliyan 6.6 kan sayen datar waya a cikin shekara ɗaya
An ƙididdige wannan adadi ne bisa bayanan yawan amfani da intanet da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta fitar, tare da amfani da matsakaicin ƙimar naira 431 kan kowane gigabyte (GB), ba wai bisa kuɗaɗen shiga da kamfanonin sadarwa suka bayyana ba.

10 Aug, 2026
Sojojin Nijeriya sun kashe Abu Khalid Al Muhajir da wasu kwamandojin ISWAP tara a Borno
Daga cikin waɗanda aka kashe har da Abu Khalid Al Muhajir, wanda aka bayyana a matsayin babban kwamandan ISWAP mai kula da samar da tawagar tsaro ta musamman da ke raka manyan jami’an ƙungiyar ta’addancin yayin zirga-zirgarsu.

10 Aug, 2026
Masarautar Kano ta musanta bidiyon da ake yadawa kan Sarki Sanusi II ya samu ‘carry-over’ a jami’a
Bidiyon, wanda ya bazu sosai a ranar Lahadi, ya yi zargin cewa tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriyar bai cika ƙa’idar cin nasarar ɗaya daga cikin darussansa ba.

9 Aug, 2026
Gwamnatin Nijeriya za ta fara sarrafa kayayyakin tsara iyali a cikin ƙasar
Yayin da yake ƙaddamar da kwamitin a Abuja, Pate ya ce jama’ar ƙasar su ne kadarar ƙasar mafi girma kuma dole a sauya su zuwa albarkatu masu samar da abubuwa da za su iya kawo ci-gaba da wadatar ƙasar.



