Duniya Zaman Lafiya

Paparoma Leo Ya Yi Kira Ga Tsagaita Wuta a Rikicin Iran da Ke Kara Tsananta a Gabas ta Tsakiya

Paparoma Leo ya yi kira da a tsagaita wuta a rikicin Gabas ta Tsakiya, yana gargadin cewa ci gaba da yaƙi na ƙara jefa fararen hula cikin wahala.

Newstimehub

Newstimehub

16 Mar, 2026

2026 03 15t122251z 423592712 rc2z4kah1j9q rtrmadp 3 iran crisis pope main

Shugaban Cocin Katolika, Pope Leo, ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a rikicin da ke kara tsananta a Gabas ta Tsakiya, musamman wanda ya shafi Iran. Ya ce ci gaba da yaƙi na jawo wa fararen hula wahala mai tsanani a yankin.

Yayin jawabi a lokacin addu’ar Angelus ta mako-mako a dandalin St. Peter’s Square da ke Vatican City, paparoman ya nuna damuwa kan abin da ya kira “mummunan tashin hankali” da ya yi sanadin mutuwar dubban fararen hula tare da tilasta wa mutane da dama barin gidajensu.

Ya bayyana cewa tsawon makonni biyu al’ummar Gabas ta Tsakiya suna fama da radadin yaƙi, yana mai kira ga shugabannin da ke cikin rikicin su dakatar da faɗa tare da komawa kan tattaunawa domin nemo mafita mai dorewa. A cewarsa, yaƙi ba zai kawo adalci, zaman lafiya ko kwanciyar hankali da mutanen yankin ke nema ba.

Paparoman ya kuma nuna damuwa kan halin da ake ciki a Lebanon, inda rikicin da ya shafi Israel da ƙungiyar Hezbollahya kara dagula matsalolin siyasa da na jin kai a ƙasar. Ya bayyana fatan cewa sabbin tattaunawa za su taimaka wa hukumomin Lebanon su samu mafita mai ɗorewa da kuma kare jin daɗin al’ummar ƙasar.

Majiyar Labari: TRT WORLD