Nijeriya

Rundunar sojin Nijeriya ta ƙuɓutar da ‘yan bautar ƙasa 47 daga ‘yan Boko Haram a Borno

Sojojin sun yi saurin ƙubutar da su daga yiwuwar garkuwar ‘yan Boko Haram/ISWAP waɗanda ke kai hare-hare yankin,’’ in ji sanarwar.

Newstimehub

Newstimehub

13 Nov, 2025

26a73c22fd49e3a70a49ccf3c4bf5d0385cb1cc674d6d9d3d3ac7a977d018f15

Rundunar Haɗin Kai ta sojojin Nijeriya (JTF) ta Arewa maso Gabashin ƙasar ta ƙuɓutar da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) su 47 daga yunƙurin garkuwar ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya a Jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar, Sani Uba ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a da ya fitar ranar Alhamis.

“An ceto ‘yan bautar ƙasa, maza 36 da mata 38, da misalin karfe 9:05 na dare a ranar Talata bayan da motocinsu suka lalace kusa da wani wuri da aka san ana garkuwa da mutane,” in ji Uba.

A cewarsa, an tura wata tawagar jami’an sintiri ta sojoji cikin gaggawa zuwa wurin bayan da wata na’urar talabijin ta CCTV da sojoji ke sa ido a kai ta gano motsin motocin bas uku a wurin da ake zargi.

“Da isowarsu, sojoji sun gano ‘yan NYSC 74 da suka makale bayan da motocinsu suka samu matsalar injin.”

Sojojin sun yi saurin kubutar da su daga yiwuwar garkuwar ‘yan Boko Haram/ISWAP waɗanda ke kai hare-hare yankin,’’ in ji sanarwar.

Kazalika, sanarwar ta kara da cewa, a yanzu haka ‘yan NYSC da aka ceto suna sansanin sojoji na Buratai kafin a ci gaba da shirye-shiryen tafiya ke su wuri mai aminci.