Nijeriya

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 60 a garin Bita na Jihar Borno

Bayanai sun nuna cewa sojojin saman sun yi amfani da jiragen yaƙi ƙirar A-29 Super Tucano domin fatattakar ‘yan ta’addan.

Newstimehub

Newstimehub

30 May, 2025

2373788f911bc280022a7dfee8088db55d710203dc27bc9a551d5de185761665

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta kashe ‘yan ta’adda aƙalla 60 bayan farmakin da dakarun Rundunar Operation Hadin Kai suka kai ta sama da kuma kasa a maboyar ‘yan ta’addan a garin Bita da ke Jihar Borno da sanyin safiyar Juma’a.

Rundunar ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a safiyar ta Juma’a.

Duk da cewa ba ta yi ƙarin haske kan yadda harin ya gudana ba, amma mai sharhi da tattara bayanai kan al’amuran tsaro a Yammacin Afirka Zagazola Makama ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun ƙaddamar da harin ne da misalin ƙarfe 1:09 na dare kan sojojin 26 Task Force Brigade.

Ya bayyana cewa nan take dakarun suka samu taimako daga sojojin sama inda aka yi ta musayar wuta har zuwa 3:23 na dare.

Bayanai sun nuna cewa sojojin saman sun yi amfani da jiragen yaƙi ƙirar A-29 Super Tucano domin fatattakar ‘yan ta’addan.

A ‘yan kwanakin nan, hare-haren Boko Haram sun dawo a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya inda ko a kwanakin baya, sai da ‘yan ta’addan suka kashe sojoji da dama a harin da suka kai wani sansanin sojoji a ƙaramar hukumar Marte ta jihar Borno.

Haka kuma a ‘yan kwanakin nan ‘yan ta’addan sun kashe fararen hula da dama a yankunan jihar waɗanda suka haɗa da manoma da ‘yan kasuwa.