A jajibirin wasan ƙarshe na Kofin Nahiyar Afirka (AFCON), an samu tashin hankali a fagen shirye-shiryen gasar bayan kocin Senegal, Pape Bouna Thiaw, ya bayyana damuwarsa kan yadda ‘yan wasansa suka isa birnin Rabat ba tare da isasshen tsaro ba, lamarin da ya jefa su cikin taron jama’a a tashar jirgin ƙasa.
Thiaw ya ce ‘yan wasan Senegal sun iso Rabat daga Tangier ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba, inda taron jama’a ya kewaye su a tashar jirgin ƙasa. Wannan ya sa ya zargi masu shirya gasar da sakaci, yana cewa rayukan ‘yan wasan sun shiga haɗari. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta kuma fitar da sanarwa tana korafi kan rashin tsaro, masauki da wuraren atisaye, tana mai cewa irin wannan matsala na iya bata martabar gasar AFCON da hoton nahiyar Afirka gaba ɗaya.














