Afirka

Shugaban Burkina Faso Traore ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar ƙawance ta ƙasashen AES

Ƙasar Mali da Burkina Faso da kuma Nijar sun buƙaci a hada kai wajen “aiwatar da manyan ayyuka” kan ‘yan ta’adda

Newstimehub

Newstimehub

24 Dec, 2025

0d6e3f1cdd8509002f512b51e583d01fb80dbc0aa8e0b23b018aad557c6ec889 e1766606377963

Shugaban Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar ƙawancen ƙasashen Sahel (AES), inda ya yi alkawarin ɗaukar manyan matakai bayan kafa rundunar haɗin gwiwa domin yaƙi da ta’addanci.

Shugaban Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traoré ya karɓi shugabancin ƙungiyar ƙawancen ƙasashen Sahel (AES) da ta ƙunshi Mali, Burkina Faso da Nijar, yana mai bayyana cewa bayan kaddamar da rundunar sojojin haɗin gwiwa, wajibi ne a aiwatar da manyan ayyuka a kwanaki masu zuwa domin tinkarar matsalolin tsaro da ta’addanci da suka addabi yankin.

Traoré bai yi cikakken bayani kan waɗannan matakai ba a jawabinsa na farko bayan nadin, amma ya jaddada aniyar ƙungiyar na ƙarfafa tsaro da farfaɗo da tattalin arziki. Ƙungiyar AES, wadda aka kafa a shekarar 2023, ta ƙunshi ƙasashe uku da ke ƙarƙashin mulkin soji, kuma a wannan shekara suka fice daga ECOWAS.

Yankin Sahel na daga cikin wuraren da suka fi fuskantar ta’addanci a duniya, inda ƙungiyoyin masu alaƙa da al-Qaeda da Daesh ke ci gaba da kai hare-hare. A wani taro da shugabannin ƙasashen suka gudanar, sun amince da ƙarfafa haɗin kai, tare da ɗaukar matakin korar sojojin ƙasashen waje, musamman na Faransa da Amurka.

Ƙungiyar AES, wadda ke da yawan jama’a kusan miliyan 78, na neman cikakken ’yancin kai da haɗin gwiwa a fannoni daban-daban, tare da kiran a aiwatar da manyan ayyuka na bai ɗaya domin murƙushe ’yan ta’adda a yankin.

Majiyar Labari: Trt Hausa