Shugaban Egypt, Abdel Fattah al‑Sisi, ya isa Saudi Arabia a wata ziyarar da aka bayyana a matsayin ta ‘yan’uwa. An tarbe shi a Jeddah inda Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, ya karɓe shi.
Sanarwar fadar shugaban Masar ta ce ziyarar na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa dangantakar tarihi tsakanin ƙasashen biyu, tare da ci gaba da tuntuba kan batutuwan yankin da na duniya da suke da muhimmanci ga ɓangarorin.
Ba a bayyana tsawon ziyarar ba, amma ta zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke nuna shirin ƙaddamar da aikin haɗa wutar lantarki tsakanin Masar da Saudiyya.
Majiyar Labari: TRT WORLD














