Mawakin Afrobeats ɗan Najeriya, Skales, ya bayyana cewa aikinsa na kiɗa ya samu sabon ƙarfi ne bayan wani bidiyo da tauraron ƙwallon ƙafa na Barcelona, Lamine Yamal, ya yi yana rawa da ɗaya daga cikin wakokinsa, lamarin da ya bazu sosai a shafukan sada zumunta.
Bidiyon da Yamal ya yi yana rawa da wakar “Shake Body” ta shekarar 2015 ya jawo hankalin jama’a a faɗin duniya, inda hakan ya sake dawo da sha’awar mutane kan kiɗan Skales tare da buɗe masa sabbin damammakin aiki.
Da yake jawabi a Harvesters Church, Skales ya bayyana farkon shekarar 2025 a matsayin lokaci mai tsanani ta fuskar ibada, inda ya shiga addu’o’i da azumi fiye da yadda ya taɓa yi a baya. Ya ce a wannan lokaci ya kai kukansa ga Allah saboda yadda yake jin ana raina aikinsa da kuma yadda harkar kiɗansa ta yi rauni.
Skales ya bayyana cewa ya rubuta abubuwan addu’a guda bakwai, kuma abin mamaki duk sun cika a rana guda. Ya ce abin da ya fi sauya masa rayuwa shi ne lokacin da Lamine Yamal ya yi rawa kaɗan da wakarsa, wanda cikin kankanin lokaci ya bazu ya zama bidiyo mai yaduwa (viral) a duniya.
A cewarsa, wannan bidiyo ya zama mahimmiyar juyawa a aikinsa, inda ya sake dawowa cikin hasken fagen kiɗa bayan wani lokaci na ja da baya.
Baya ga haka, Skales ya samu manyan gayyata, ciki har da kira domin yin waka a bikin Copa del Rey na kulob ɗin Barcelona, ɗaya daga cikin manyan tarukan ƙungiyar.
Haka kuma, domin tunawa da wannan lokaci mai tarihi, Skales ya fitar da sabuwar waka mai taken “Dance Like Lamine Yamal”, wadda ke murnar bidiyon da ya taimaka wajen farfaɗo da aikinsa a masana’antar kiɗa.














