Nijeriya

Sojojin Nijeriya sun kama wasu da ake zargin masu kai wa ’yanta’adda kayayyaki ne a Jihar Yobe

Rundunar ta ce an gudanar da aikin ne ranar Talata, 8 ga Satumba, bayan samun bayanan sirri kan wasu kayayyakin da ake zargin za a wuce da su zuwa ga ’yanta’addan da ke aiki a yankin Yunusari-Mobbar.

Newstimehub

Newstimehub

9 Sep, 2026

b62fe0d0 e949 4569 9805 67635138bd2d 1777388191620

Rundunar Sojin Nijeriya ta kama wasu mutane biyu da ake zargin masu samar wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP kayayyaki ne a Jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar, kana ta ƙwato ɗimbin kayayyakin gyaran babura.

Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedkwatar Rundunar Hadin Gwiwa ta yankin Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, inda ta ce an gudanar da aikin ne ranar Talata, 8 ga Satumba, bayan samun bayanan sirri kan wasu kayayyakin da ake zargin za a wuce da su zuwa ga ’yanta’addan da ke yankin Yunusari-Mobbar.

Dakarun Bataliya ta 159 da ke aiki ƙarƙashin Sashi na Biyu na Operation HADIN KAI, tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro ne suka kama kayayyakin a Gadar Gumsa da ke ƙaramar hukumar Geidam, a cewar sanarwar.

Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da tayoyin babura da ƙarafan injina da man inji da sassan birki, da sauran kayayyakin gyaran babura.

Kazalika dakarun sun kuma ƙwato takalma guda 145 da wayoyin hannu guda biyu, da wasu kayayyakin amfani.

An miƙa waɗanda ake zargin da kayayyakin da aka ƙwato ga Rundunar Leken Asiri ta 27 ta Sojin Nijeriya domin gudanar da ƙarin bincike da ɗaukar matakan da suka dace, in ji sanarwar.

Rundunar Operation HADIN KAI, ta ce kamen wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi na tarwatsa hanyoyin samar da kayayyaki ga ƙungiyoyin ta’addanci tare da hana su samun abubuwan da suke buƙata domin gudanar da ayyukansu.

Ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa ayyukan yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.