Gwamnatin Tanzania na shirin sanya hannu kan wata babbar yarjejeniya ta gina tashar tace iskar gas (LNG) da za ta lashe dala biliyan 42 kafin watan Yuni, a wani mataki da ake ganin zai sauya tattalin arzikin ƙasar gaba ɗaya tare da maida yankin Gabashin Afirka cibiyar fitar da iskar gas zuwa kasuwannin Asiya.
Ministan tsare-tsare da zuba jari na ƙasar, Kitila Mkumbo, ya ce tattaunawar kasuwanci ta kammala, abin da ya rage kawai shi ne tsarin doka. Kamfanonin Equinor da Shell ne ke jagorantar aikin, tare da haɗin gwiwar Exxon Mobil, Pavilion Energy, Medco Energi da kamfanin man fetur na ƙasa TPDC. Aikin zai buɗe tanadin iskar gas mai girman cubic feet tiriliyan 47, kuma ana sa ran zai samar da ayyukan yi sama da 100,000, tare da fara samarwa cikin shekaru takwas masu zuwa.
Ministan ya kuma bayyana cewa shugaban ƙasa Samia Suluhu Hassan ta umarci babban bankin ƙasa da ya sayar da wani ɓangare na zinari domin samun kuɗin kammala manyan ayyukan more rayuwa, a daidai lokacin da wasu ƙasashen Turai suka dakatar da tallafin kuɗi sakamakon rikicin zaɓen shekarar da ta gabata.














