Bola Ahmed Tinubu ya karɓi wata babbar tawagar sojoji da diflomasiyya ta Amurka a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, a wani bangare na ci gaba da tattaunawa tsakanin Najeriya da Amurka kan haɗin gwiwar tsaro. Tawagar ta Amurka ta zo ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban United States Africa Command (AFRICOM), Janar Dagvin Anderson, tare da manyan jami’an tsaro da diflomasiyya.
Bayanan taron sun fito ne daga Mataimakin Mai Taimaka wa Shugaban Kasa kan Kafafen Sadarwa, Dada Olusegun, wanda ya wallafa su a shafin X. A cewarsa, Shugaba Tinubu ya gana da tawagar AFRICOM tare da Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Kasa, Mallam Nuhu Ribadu, da kuma shugabannin manyan rundunonin tsaro da hukumomin leƙen asiri na Najeriya.
Daga bangaren Amurka, taron ya haɗa da Janar Anderson, Babban Jami’in Sojoji na AFRICOM Garric M. Banfield, Babban Mashawarcin Harkokin Waje Ambasada Peter Vrooman, da sauran mambobin tawagar. Haka kuma, Mukaddashin Jakadan Amurka a Najeriya, Keith Heffern, ya halarci ganawar.
A bangaren Najeriya kuwa, Shugaban Kasa ya kasance tare da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), da shugabannin rundunonin soji da na leƙen asiri. Taron ya jaddada aniyar bangarorin biyu na ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro da musayar bayanai domin fuskantar kalubalen tsaro a yankin.
Majiyar Labari: TVC NEWS














