Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya sa hannu kan wata doka da ta tanadi tura duk kuɗaɗen shiga daga mai da gas na NNPC kai-tsaye cikin asusun gwamnatin tarayya. Shugaban ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmin mataki da nufin inganta tafiyar da kuɗaɗen ƙasa.
Sabuwar dokar ta kawo ƙarshen wasu tanade-tanade da ke bai wa NNPCL damar riƙe kaso daga ribar mai da gas domin gudanarwa da bincike. A yanzu, duk kuɗaɗen shiga, ciki har da haraji da kudaden lasisi, za su rika shiga asusun gwamnati kai-tsaye.
Haka kuma hukumomin da ke kula da ɓangarorin mai, kamar NUPRC da NMDPRA, za su miƙa kuɗaɗen da suke samu zuwa asusun tarayya, yayin da za a rika ware musu kuɗaɗen aiki ta hanyar kasafin kuɗi. Gwamnati ta ce matakin zai taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga da rage gibi.
Fadar shugaban ƙasa ta ce tsoffin cire-cire da dokar ta amince da su sun rage kuɗaɗen shiga sosai, lamarin da ya shafi matakan kuɗi a matakan tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi. Tinubu ya kuma umarci sake nazari da kafa kwamiti domin aiwatar da sauye-sauyen.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














