Duniya

Trump na so a kawo ƙarshen yaƙin Iran ta diflomasiyya, Netanyahu ya ce a kai ƙarin hare-hare: rahoto

Wata tattaunawa ta waya ta bayyana bambancin ra’ayi tsakanin shugabannin biyu kan Iran, inda Washington take neman bai wa tattaunawar da ake yi ƙarin lokaci domin ta cim ma nasara, in ji wani rahoton wata kafar watsa labaran Amurka.

Newstimehub

Newstimehub

2 Nov, 2026

d6b98b06 7477 4e08 a544 b5c66781ae7d 1793565731280

Shugaban Amurka Donald Trump ya fi ba da fifiko ga tattaunawar diflomasiyya da Tehran duk da mastin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yake yi na ƙaddamar da sabbin hare-haren soji nan-take bayan zaɓukan tsakiyar wa’adi na Amurka na ranar Talata, in ji wani rahoton kafofin watsa labaran Amurka.

A wata tattaunawa ta waya ta ranar Asabar, shugaban Isra’ila ya matsa wa Washington ta kai sabbin hare-haren soji kan Iran da zarar an kammala zaɓen, amma Trump ya fi mayar da hankali kan ba da dama ga tattaunawar diflomasiyyar da ake yi, in ji majiyoyi na Amurka da Isra’ila da ke da masaniya game da musayar ra’ayin, kamar yaɗa kafar Axios ta ruwaito ranar Lahadi.

Netanyahu ya “damu” game da hanyar da Trump ke bi, in ji majiyoyi.

Jami’in Isra’ilan ya kuma bayyana tattaunawar a matsayin “tsauri,” yayin da majiyar Amurka ta bayyana ta a matsayin “na ƙeƙe-da-ƙeƙe.”

Trump ya shaida wa manema labarai cewa ya tattauna da Netanyahu game da Iran ranar Asabar, yana mai cewa sun yi wata tattaunawa “mai tsabar kyau”

A baya dai, Shugaban Amurkan ya ce tattaunawa da Tehran na tafiya yadda ya kamata, yana mai ƙarawa da cewa shi ba ya “cikin gaggawa” don fara kai hare-hare, duk da cewa a baya ya bayyana fara kai hare-hare bayan ranar 3 ga watan Nuwamba.

An zafafa ƙoƙarin diflomasiyya

Matsin da Netanyahu yake yi na sabunta kai hare-hare na zuwa ne a cikin ƙoƙarin farfaɗo da tattaunawa a hukumance, biyo bayan saƙon da mataimakin shugaban ƙasar Amurka JD Vance ya tura wa Mohsen Rezaei, sakataren majalisar ƙoli ta tsaron Iran, kan yiwuwar sake fara tattaunawa a hukumance.

A wani ɓangaren kuma, masu shiga tsakani na Qatar suna tattaunawa da wakilan Iran domin samar da komawa kan teburin tattaunawa kai-tsaye.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargaɗin cewa yarjejeniya ta kasance tana jiran amsoshi daga Amurka, yana mai cewa babu wata tsayayyiyar yarjejeniya kawo yanzu.

Fadar White House da ofishin Firayim Ministan Isra’ila sun ƙi yin toskaci kan rahoton, in ji Axios.