Shugaban Amurka Donald Trump ya amince cewa Musulmi na daga cikin waɗanda ake kashewa a Najeriya, yayin da ya sake jaddada barazanar cewa Amurka na iya ƙara kai hare-haren sama idan rikicin tsaro ya ci gaba.
Trump ya bayyana hakan ne bayan sojojin Amurka sun kai hari a Sokoto a ranar Kirsimeti, inda suka jefa bama-bamai kan sansanonin ƙungiyar jihadi Lakurawa, a wani yanki da galibinsa Musulmi ne. Harin ya zo ne kusan wata guda bayan Trump ya yi barazanar tura sojojin Amurka zuwa Najeriya domin, a cewarsa, kare Kiristoci da ake kashewa.
A wata hira da Jaridar New York Times, Trump ya ce yana fatan harin ya zama sau ɗaya, amma ya ƙara da cewa idan kisan Kiristoci ya ci gaba, to Amurka za ta iya sake kai wasu hare-hare. Sai dai ya amince cewa Musulmi ma na rasa rayukansu a rikicin, kodayake ya ce “an fi kashe Kiristoci.”
Gwamnatin Najeriya ta ci gaba da musanta ikirarin cewa ana kai wa Kiristoci hari ne kawai, tana mai cewa rikicin tsaron ya shafi dukkan ‘yan ƙasa ba tare da bambancin addini ba. Duk da haka, ta bayyana shirinta na haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin magance matsalar tsaro.
Harin na Amurka ya jawo martani daga kasashen duniya, inda Paparoma Leo XIV ya yi Allah wadai da hare-hare kan ƙasashe masu ‘yancin kai, yana sukar Amurka da wasu manyan ƙasashe kan irin waɗannan matakai.














