A yayin da rikicin da ya daɗe yana gudana kan madatsar ruwa ta Grand Ethiopian Renaissance Dam ke ci gaba da tayar da hankula a yankin Gabashin Afirka, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana ganin akwai damar cimma matsaya ta hanyar tattaunawa tsakanin Masar da Habasha domin kauce wa rikici da tabbatar da adalcin rabon ruwan kogin Nilu.
Trump ya ce madatsar ruwan GERD na toshe kwararar Nilu, abin da ke barazana ga Masar da Sudan waɗanda suka dogara da kogin tsawon dubban shekaru. Da yake karɓar baƙuncin Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi, ya ce zai yi ƙoƙarin dawo da tattaunawa kan hanya domin warware sabanin da ke tsakaninsu da Habasha kan cika da sarrafa madatsar.
Habasha ta kaddamar da madatsar a Satumbar 2025 bayan gini na tsawon shekaru 14, yayin da Masar da Sudan ke neman yarjejeniya ta doka da za ta tabbatar da adalcin rabon ruwa.














