A gaban manyan shugabannin kamfanoni da jagororin duniya a taron tattalin arzikin duniya na Davos, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana ƙasarsa a matsayin ginshiƙin da tattalin arzikin duniya ke dogaro da shi, yana mai jaddada cewa sauye-sauyen da ya kawo sun jawo gagarumin farfaɗo da tattalin arzikin Amurka.
Da yake jawabi a WEF 2026, Trump ya ce Amurka ce “injin tattalin arzikin duniya,” yana mai ikirarin cewa cikin shekara guda bayan dawowarsa Fadar White House, hauhawar farashi ta ragu, zuba jari ya karu, ayyukan yi sun yawaita, kuma tattalin arziki na bunƙasa fiye da hasashen IMF.
Ya ce an samu jarin kusan dala tiriliyan 20, kuma ci gaban tattalin arziki ya haura kashi 4.6 a zangon karshe na 2025. Sai dai kalamansa sun zo ne a lokacin da ake samun takaddama tsakaninsa da kasashen Turai kan batun Greenland, inda ya yi barazanar kakaba haraji kan wasu ƙasashen da ke goyon bayan Denmark, lamarin da ya jawo suka daga shugabannin Turai da NATO.














