Gwamnatin Turkiyya ta isar da tantuna 10,000 daga cikin 30,000 da ta yi alkawarin kai wa Sudan, domin taimakawa wajen rage matsalar ƙarancin matsugunai da rikicin ƙasar ya haifar. Jirgin kayan agajin ya isa Port of Sudan, inda jami’an AFAD na Turkiyya da jakadan ƙasar a Sudan, Fatih Yıldız, tare da manyan jami’an Sudan da na ƙungiyoyin agaji suka tarbe shi.
An ɗauko tantunan ne daga tashar Mersin ta Turkiyya a ranar 6 ga Disamba, kuma za a raba su zuwa jigila uku. Hukumar ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) tare da AFAD da gwamnatin Sudan za su kula da rarraba su ga mutanen da suka fi buƙata, musamman a yankunan Darfur ta Arewa da Kordofan.
Jakadan Turkiyya ya bayyana cewa agajin ba kayan taimako kaɗai ba ne, har ila yau yana nuna goyon baya da ƙaƙƙarfan zumunci tsakanin Turkiyya da Sudan. Jami’an Sudan da na IOM sun yaba da tallafin, suna mai tabbatar da cewa za a raba kayan cikin gaskiya da tsari zuwa ƙauyuka da sansanonin ’yan gudun hijira.
Majiyar labari: Trt Hausa














