Ƙasashen Afrika kudu da hamada na shirin fuskantar jerin manyan zaɓuka a shekarar 2026, inda al’ummomi za su fita rumfunan zaɓe domin zaben shugabanni, ‘yan majalisa da sauran shugabannin gwamnati a lokuta da dama cikin yanayin matsin tattalin arziki da siyasa.
A Uganda, ana gudanar da zaɓen gama-gari domin zaben shugaban ƙasa da ‘yan majalisa, inda Shugaba Yoweri Museveni ke neman wa’adi na bakwai bayan ya shafe tun 1986 kan mulki. Daya daga cikin manyan masu kalubalantarsa shi ne Bobi Wine, wanda ya zo na biyu a zaɓen 2021.
A Jamhuriyar Congo kuma, ana sa ran gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a watan Maris, inda Shugaba Denis Sassou Nguesso ke neman sake tsayawa takara duk da tsawon shekarunsa a mulki. A Benin, zaɓen shugaban ƙasa zai gudana a watan Afrilu, inda Shugaba Patrice Talon ba zai sake tsayawa takara ba.
Ethiopia za ta gudanar da zaɓen ‘yan majalisa a watan Yuni, yayin da ake ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu yankuna. A Zambia kuma, ana sa ran zaɓen gama-gari a watan Agusta, inda Shugaba Hakainde Hichilema ke neman wa’adi na biyu.
Gambia za ta yi zaɓen shugaban ƙasa a watan Disamba, inda Shugaba Adama Barrow ke neman wa’adi na uku, lamarin da ya janyo muhawara bayan gazawar sabon kundin tsarin mulki. A Sudan ta Kudu, ana sa ran gudanar da zaɓe na farko tun bayan samun ‘yancin kai, duk da jinkiri da rashin kammala wasu muhimman shirye-shirye.
Sauran ƙasashe kamar Cape Verde, Djibouti, Sao Tome da Principe da Kamaru ma suna shirin gudanar da zaɓuka, duk da cewa wasu lokutan ba a tabbatar da su ba tukuna.
Masu sa ido na cikin gida da na ƙasashen waje na sa ran waɗannan zaɓuka za su zama gwaji ga dimokiraɗiyya da zaman lafiyar yankin a shekarar 2026.














