An kammala wasannin kwata fainal na AFCON 2025, inda Nijeriya za ta fafata da Maroko a wasan dab da ƙarshe, yayin da Masar kuma za ta gwabza da Senegal bayan ta fitar da masu riƙe da kofin, Ivory Coast.
Masar ta doke Ivory Coast da ci 3-2 a Agadir, inda Omar Marmoush da Ramy Rabia suka ci ƙwallaye biyu a farkon wasa, kafin Mohamed Salah ya ƙara ta uku bayan hutun rabin lokaci. Duk da ƙoƙarin Ivory Coast na rage gibin, Masar ta tsare nasarar.
Da wannan sakamakon, Masar za ta kara da Senegal a wasan dab da ƙarshe a ranar Laraba a Tangier. Kocin Masar, Hossam Hassan, ya yaba wa ’yan wasansa, yana mai cewa sun nuna kishin ƙasa da ƙwazo.
A ɗaya ɓangaren kuma, Victor Osimhen ya sake haskakawa yayin da Nijeriya ta doke Aljeriya 2-0 a Marrakesh. Osimhen ya ci ƙwallo ɗaya da kansa, sannan ya bayar da taimako aka ci ta biyu ta hannun Akor Adams.
Osimhen, wanda ya zama gwarzon ɗan wasa a wasan, ya ce nasarar ta samo asali ne daga haɗin kan tawagar baki ɗaya. Nijeriya yanzu za ta fafata da Maroko, mai masaukin baƙi, a wasan dab da ƙarshe.
Kocin Nijeriya, Eric Chelle, ya bayyana Maroko a matsayin ƙungiya mai ƙarfi, amma ya ce Super Eagles za su yi duk mai yiwuwa domin cimma burin lashe kofin nahiyar karo na huɗu.













