Duniya

Xi da Trump sun amince Mashigar Hormuz ta ci gaba da kasancewa a buɗe

A halin da ake ciki, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi da takwaransa na China Xi “sun yi tattaunawa da ganawa mai matukar kyau da amfani,” yana mai cewa abubuwan da suka tattauna “duk sun amfanar da kasashen biyu.”

Newstimehub

Newstimehub

14 May, 2026

dc680299089b855b6b3ae01a30bf9c56ca1b32750a0693359164b3d480ba29eb main

Shugaban Amurka Donald Trump da shugaban ƙasar China Xi Jinping sun amince cewa “dole Mashigar Ruwan Hormuz ta kasance a buɗe,” in ji Fadar White House bayan taron kolin Amurka da China da aka gudanar a Beijing.

Fadar White House ta ce a wata sanarwa da ta wallafa a shafin X cewa, “Shugaba Trump ya yi kyakkyawan taro da Shugaba Xi na China.”

Sanarwar, wadda aka fitar a ranar Alhamis, ba ta yi magana kan batun Taiwan ba, amma ta fi mayar da hankali kan yakin Iran da kuma batun Mashigar Hormuz.

“Bangarorin biyu sun amince cewa dole ne Mashigar Hormuz ta kasance a buɗe domin tabbatar da ‘yancin zirga-zirgar makamashi. Shugaba Xi ya kuma bayyana adawar China ga mayar da Mashigar wurin soji ko ƙoƙarin kakaba kuɗin amfani da shi, sannan ya nuna sha’awar sayen ƙarin mai daga Amurka domin rage dogaro da mashigar a nan gaba.”

“Duka ƙasashen sun kuma amince cewa Iran ba za ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba,” in ji sanarwar.

Bugu da ƙari, Fadar White House ta ce bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin ƙara haɗin gwiwar tattalin arziki, “ciki har da faɗaɗa damar kasuwanci ga kamfanonin Amurka a China da kuma ƙara zuba jarin China a masana’antunmu. Manyan shugabannin kamfanoni na Amurka da dama sun halarci wani ɓangare na taron.”

Trump ya kuma jaddada buƙatar ci gaba da matakan dakile shigar sinadaran fentanyl zuwa Amurka, da kuma ƙara sayen kayayyakin amfanin gona daga Amurka, in ji sanarwar.

Trump da Xi a kan taron

A halin da ake ciki, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi da takwaransa na China Xi “sun yi tattaunawa da ganawa mai matukar kyau da amfani,” yana mai cewa abubuwan da suka tattauna “duk sun amfanar da kasashen biyu.”

Ya kuma gayyaci Xi da matarsa ta farko ta China zuwa ziyara a Amurka a ranar 24 ga Satumba, yana kiran dangantakarsu ta “musamman sosai.”

A nasa bangaren, Shugaban China Xi Jinping ya ce dangantakar China da Amurka ita ce mafi “muhimmanci” a duniya, yana cewa ta kasance “mai dorewa” kuma “dole mu sa ta yi aiki kuma kada mu lalata ta.”

‘Batu mafi muhimmanci’

Tashin hankali a yankin ya ci gaba da kasancewa mai zafi tun bayan harin Amurka da Isra’ila kan Iran a farkon wannan shekara wanda ya jawo martani na soji daga Iran da kuma rugujewar zirga-zirga a kusa da hanyar ruwa ta Hormuz, wata muhimmiyar hanyar ruwa tsakanin Oman, Iran da UAE wadda ke hade tekun Gulf da na Oman.

A cikin yanayin wata yarjejeniya mai rauni ta tsagaita wuta, Amurka ta kuma aiwatar da dakatar da zirge-zirgar jiragen ruwa na Iran a hanyar ruwa ta Hormuz tun daga 13 ga Afrilu.

A cewar wata sanarwa ta hukuma ta China, Xi ya shaida wa Trump cewa “kasashen biyu za su iya samun rashin fahimta har ma da rikici,” idanba a bi batun Taiwan yadda ya kamata ba.

“Batun Taiwan shi ne mafi muhimmanci a cikin alakar China da Amurka. Idan aka bi da ita yadda ya kamata, dangantakar kasashen biyu za ta ci gaba cikin kwanciyar hankali,” in ji Xi.

“In ba haka ba, kasashen biyu za su sami matsala har ma da rikice-rikice, wanda zai sanya dukkan dangantakar cikin babbar hadari,” in ji gargadin shugaban kasar China ga takwaransa na Amurka.

Dangantakar tattalin arzikin tsakanin kasashen, wadda ta kai dala biliyan 414 a bara, “mai amfani ce ga juna kuma mai riba ga kowa,” in ji Xi, yana kara cewa ya “yarda” da Trump a kan “sabon hangen nesa na gina dangantakar China-Amurka mai amfani da zaman lafiyar dabaru.”