Wannan furuci nasa ya zo ne a daidai lokacin da jakadan Amurka Steve Witkoff da Jared Kushner, surukin Shugaba Donald Trump, suke Moscow domin tattaunawa mai mahimmanci kan kawo ƙarshen yaƙin da ya kusan cika shekaru huɗu, bayan kwanaki na ƙoƙarin diflomasiyya mai zafi. “Ba mu da niyyar yaƙi da Turai, amma idan Turai ta fara yaƙi, mu a yanzu nan mun shirya,” in ji Putin ga manema labarai a Moscow.
Ya ƙara da cewa, “Ba su da ajandar zaman lafiya, suna gefen yaƙi,” yana maimaita zargin cewa shugabannin Turai na hana ƙoƙarin Amurka na sasanta rikicin Ukraine. Putin ya bayyana cewa canje-canjen da Turai ta yi wa sabon shirin Trump na kawo ƙarshen yaƙin “sun nufa ne da wani abu guda — hana duk wani yunƙurin zaman lafiya gaba ɗaya tare da gabatar da buƙatun da Rasha ba za ta taɓa amincewa da su ba.” Amurka ta gabatar da tsarin matakai 28 domin kawo ƙarshen rikicin, sannan daga baya aka gyara shi bayan suka daga Kyiv da Turai, waɗanda suka ce yana ɗauke da shawarwarin da suka fi fifita Rasha.
Shirin na Trump na neman kawo ƙarshen yaƙin ya fusata ƙasashen Turai, domin suna tsoron hakan zai tilasta Ukraine mika wuya ga buƙatun Rasha — musamman kan iyakoki da yankuna. Turai, saboda tsoron ƙarin barazanar Rasha, ta jaddada cewa ba za a kakabawa Ukraine zaman lafiya mara adalci ba. Yanzu haka, jakadan Trump na ƙoƙarin kammala tsarin tare da samun amincewar Moscow da Kyiv.














