A wani mataki da ke nuna ƙara ɗaurewar zumunci da haɗin kai, shugabannin Mali, Burkina Faso da Nijar sun haɗu a Bamako domin buɗe sabuwar tashar watsa labarai ta kawancen kasashen Sahel (AES). Wannan sabon shiri na kafofin watsa labarai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen ke ƙoƙarin gina murya ɗaya da za ta wakilci muradunsu a yankin Sahel.
A yayin taron na biyu na kawancen AES da aka gudanar a Bamako, Shugaban Mali Janar Assimi Goita, Shugaban Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore da Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani sun kaddamar da gidan Talabijin na AES. A cewar sanarwar hukuma, an kafa tashar ne domin yaƙi da labaran ƙarya da kuma ƙarfafa labaran yankin daga mahangar kasashen Sahel.
Taron na kwanaki biyu ya mayar da hankali ne kan nazarin nasarorin shekara ta farko tun bayan kafuwar AES a 2024, tare da duba manyan ƙalubalen da kawancen ke fuskanta. Wannan ya zo ne bayan ficewar kasashen uku daga ECOWAS a watan Janairu.
Haka kuma, shugabannin sun tattauna kan ci gaban rundunar haɗin gwiwa ta AES (FU-AES), wadda ke shirin tura sojoji kusan 5,000 domin yaƙar ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai. An kuma bayyana rawar Bankin Zuba Jari da Ci Gaba na AES (BCID-AES) da aka kafa da jarin CFA biliyan 500 domin tallafa wa ayyukan more rayuwa, makamashi da noma.














