Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta zartar da dokar tilasta wa ‘yan ƙasa shiga aikin soja domin kare ƙasar daga barazanar tsaro daga ciki da wajen ƙasa. An amince da dokar ne a Taron Majalisar Ministoci da Shugaba Janar Abdourahamane Tiani ya jagoranta.
Dokar ta tanadi cewa ‘yan ƙasa su amsa kiran fagen yaƙi cikin gaggawa idan an buƙaci hakan, su kuma bai wa hukumomi rahoto idan sun ga baki masu barazana. Haka kuma, an haramta duk wata sadarwa da za ta iya kawo cikas ga ayyukan tsaro.
Gwamnatin na shirin ƙaddamar da shirin wayar da kan jama’a a faɗin ƙasar domin ƙarfafa kishin ƙasa da bayyana rawar da jama’a za su taka wajen kare Nijar.
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da Nijar ke fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda a yankin Sahel, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakaninta da Mali da Burkina Faso ta ƙungiyar AES, wadda ta kafa rundunar soji ta haɗin gwiwa mai ƙarfin sojoji 5,000 domin yaƙi da ta’addanci da kare iyakoki.














