Bayan samun sabuwar sarauta da ta jawo hankalin jama’a, fitaccen mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya bayyana aniyarsa ta amfani da wannan muƙami domin haɗa kan mawaƙan Hausa da kuma ɗaga martabar sana’ar waƙa. A cewarsa, wannan sarauta ba ta tsaya kan suna kaɗai ba, illa wata dama ce ta kawo sauyi mai ma’ana a harkar waƙa a ƙasar Hausa.
Rarara ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce zai buɗe fadarsa ta sarauta tare da naɗa hakimai da wakilai da za su taimaka masa wajen tafiyar da harkokin sarautar. Wannan ya biyo bayan naɗinsa da Sarkin Daura, Umar Faruq, ya yi masa a matsayin Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa, a wani gagarumin biki da aka gudanar a fadar sarkin Daura a jihar Katsina.
Mawaƙin ya ce ya ji daɗin wannan muƙami matuƙa, yana mai cewa yadda jama’a suka karɓi sarautar ne ya fi ba shi farin ciki. Ya kara da cewa sarautar ta buɗe masa idanu kan yadda rayuwa take juyawa, daga yadda ya taso har zuwa matakin da ya kai a yanzu.
Rarara ya bayyana cewa duk da mahaifinsa yana fata ya fi ‘yan uwansa karatu, Allah Ya ƙaddara masa waƙa a matsayin hanyar rayuwa. Ya kuma ce akwai mutane da dama da ke sha’awar wannan sarauta, amma sarkin Daura ya duba cancanta da tasirin aikinsa kafin ya yanke hukunci.
A cewarsa, sarautar Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa ta bambanta da sauran sarautun waƙa na masarautu, domin tana wakiltar muryar mawaƙan Hausa baki ɗaya, ciki har da na Najeriya da sauran sassan Afirka. Ya ce duk da girmamawa ga sauran mawaƙa masu sarauta, wannan muƙami nasa na da faɗi da nauyi na musamman.
Rarara ya ƙara da cewa zai buɗe makarantar koyon waƙa, ya haɗa gwiwa da masana harkar Hausa, tare da ɗaukar duk matakan da suka dace domin bunƙasa sana’ar waƙa, yana mai fatan dukkan mawaƙa za su amfana da wannan sarauta da yardar Allah.














