Duniya Filistin

Kiristocin Falasɗinu sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a Gaza da Gaɓar Yamma bayan dogon tsaiko

Kiristocin Falasɗinu sun koma gudanar da bukukuwan Kirsimeti a Gaza da Gaɓar Yamma karo na farko tun Oktoban 2023, duk da lalacewar wurare da kuma halin ƙunci da ake ciki.

Newstimehub

Newstimehub

25 Dec, 2025

5a01c63570bfc0468c7cbb56069a1011ed6194d83aedf7c7aecb18a4dbd093a6 e1766659763960

Dubban Kiristocin Falasɗinu sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a bainar jama’a a Gaza da aka yi wa ƙawanya da kuma Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, a karon farko tun bayan fara rikicin kisan-ƙare-dangi a watan Oktoban 2023.

A cikin shekaru biyu da suka gabata, an dakatar da bukukuwan Kirsimeti a Gaza sakamakon hare-haren Isra’ila. A Gaɓar Yamma kuwa, ko dai an rage bukukuwan ko an soke su gaba ɗaya domin nuna goyon baya ga Falasɗinawan da ke cikin mawuyacin hali a Gaza.

A birnin Bethlehem, wurin da aka fi danganta da haihuwar Annabi Isa (A.S), dubban mutane sun cika tituna suna gudanar da tattaki da shagulgula cikin nishadi, inda aka ga masu sanye da kayan Santa Claus suna kaɗe-kaɗe da raira waƙoƙin Kirsimeti.

A Gaza kuma, Kiristoci Falasɗinawa sun gudanar da bukukuwansu a Cocin Iyali Mai Tsarki, wadda ta lalace sakamakon hare-haren Isra’ila, kuma ta zama mafaka ga Falasɗinawa da dama da aka raba da muhallansu.

Wannan biki na Kirsimeti shi ne na farko da Kiristocin Gaza suka gudanar tun ranar 7 ga Oktoba, 2023, bayan da hare-haren Isra’ila suka tilasta dakatar da duk wani babban biki a Gaza da Gaɓar Yamma.

438c391dfc3db09312aa72a8772bc68f21076a235aad0398b03125f5bd1559f4 1 2
472baab1043cbccbb673dce42c3106266075a07240de93a2679e7598294613f1 1 2
bcfacba177c7d142d62c46f933cf2778900cdfd053b7fa0485e27ea7239b8364 1 2
3c25c153092a99a2f57572b40c8c5c129568e3a58a68d6cc18a44273cb7c150f 1 2
ad89ba7d10063fdbf78f2f2c033f402555cda6cd57e27199bb11409b20efd965 1 2
71ba7d1430add13a4a677dd4bcf2d1142d60dd3bc8fd4cc503011382d00bbbe7 1 2

Majiyar Labari: Trt Hausa