A wani gagarumin samame da ya nuna ƙoƙarin jami’an tsaro na daƙile manyan laifuka, Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta cafke mutane 22 da ake zargi da aikata manyan laifuka a jihohi daban-daban na ƙasar nan, ciki har da wani fursuna da ya tsere daga gidan yarin Kuje.
Rundunar ta ce sashen Special Tactical Squad (STS) ne ya gudanar da ayyukan bisa sahihan bayanan sirri, inda aka cafke mutanen da ake zargi da laifuka kamar fashi da makami, satar mutane, fashin dabbobi, satar mota, safarar miyagun ƙwayoyi, kwaikwayon jami’an tsaro da lalata tattalin arziƙi. A Abuja, an kama Ayo Abiodun, fursunan Kuje da ya tsere, wanda ake zargi da kai wa wani sojan Nijeriya fashi da makami.
A yayin samamen, an kwato bindigogi guda shida daban-daban, harsasai, motocin hawa, babura, miyagun ƙwayoyi da sauran kayan da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifuka. Haka kuma, an cafke wasu mutane a Kaduna–Abuja Expressway, Edo, Lagos, Ogun da Nasarawa, da ake alaƙanta su da fashi, satar mota, tayar da zaune tsaye, garkuwa da mutane da fashin shanu.
Rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da dukkan waɗanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.














