Sabbin rahotanni sun tabbatar da cewa kamfanin Meta ya sanar da cewa zai sayi kamfanin fasahar ƙirƙira Manus, wanda aka kafa a China amma ke da hedikwata a Singapore, domin ƙara ƙarfin AI a duk dandamominsa. Ba a bayyana adadin kuɗin sayen ba, amma majiyoyi sun ce darajar yarjejeniyar tana tsakanin dala biliyan $2bn zuwa $3bn.
Manus ta yi fice ne bayan ta ƙirƙiri abin da ta kira agent ɗin AI na farko a duniya, wanda ke iya yanke shawara da gudanar da ayyuka ba tare da dogon turawa ba kamar chatbot ɗin ChatGPT. Wannan ya sa aka kwatanta ta da “China’s next big AI breakthrough”, kafin daga baya ta koma Singapore saboda yanayin takaddama tsakanin China da Amurka.
Meta ta ce za ta haɗa Manus cikin manyan ayyukanta na AI, musamman Meta AI da kasuwancin WhatsApp SMB. Masana sun bayyana wannan a matsayin babbar dama ga burin Mark Zuckerberg na ƙara amfani da AI mai ‘agentic capability’ a rayuwar yau da kullum.














