Abin ya zama kamar musayar martani tsakanin Amurka da wasu ƙasashen Afirka. Bayan gwamnatin Trump ta saka Burkina Faso cikin jerin ƙasashen da aka hana shiga Amurka gaba ɗaya, ƙasar ta yanke shawarar maida martani ta hanyar dakatar da bai wa ’yan Amurka biza.
A cikin sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, an ce matakin na bin ƙa’idar ramuwar gayya, tare da jaddada cewa Burkina Faso tana mutunta dangantakar ƙasa da ƙasa bisa girmamawa da daidaito.
Mali ma ta bi sahu, inda ta sanar da cewa za ta aiwatar da irin waɗannan sharudda ga ’yan Amurka, kamar yadda Amurka ta ɗora mata. Haka kuma Nijar ta nuna irin wannan matsayi na goyon bayan ƙa’idar martani a harkokin diflomasiyya.
Wannan na zuwa ne bayan sanarwar tsohon shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya ayyana takunkumin hana shiga ƙasarsa ga wasu ƙasashe 39, mafi yawansu daga Afirka, matakin da zai fara aiki a ranar 1 ga Janairun 2026.
Majiyar Labari: TRT AFRIKA














